Accessibility links

Kwararru sun ce duk da ya ke 'yan Boko Haram na cigaba da kai hare-hare kamar yadda su ka saba, kashinsu ya kusa bushewa muddun Buhari na Shugaban Najeriya.

Kwararru ciki har da wani tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan sandan Nijeriya kuma dan Majalisar Dattawan Nijeriya a yanzu Sanata Nuhu Aliyu ya yaba da shirin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kaurar da hedikwatar Rundunar Sojin Najeriya daga Abuja zuwa Maiduguri har sai an gama yaki da Boko Haram. Ya ce duk da cewa har yanzu Boko Haram na kai hare-hare a sassan arewacin Najeriya, gwamnatin Janar Buhari ta kama hanyar magance matsalar kuma ga dukkan alamu za ta yi nasara.

Sanata Aliyu y ace sam ‘yan Boko Haram ba Musulmi ba ne saboda abubuwan da su ke yi sun saba ma addinin Musulunci. Sanata Aliyu, wanda ke jawabi a wani taron shekara-shekara na wani kwamitin Fadakarwa kan addanin Musulunci a Masarautar Kwantagora ta jihar Naija. Ya ce akwai matukar bukatar kungiyoyin addinin Musulunci su rika amfani da tsarin da addinin Musulunci ya gindaya. Y ace bai kamata a bar mutum yah au mumbari ya na ta magana da sunan addinin Musulunci ba.

Wakilinmu a Minna wanda ya aiko ma na wannan rahoton, Mustafa Nasiri Batsari ya ruwaito shugaban sashin makarantu na wannan Kwamitin Malam Nasiri Hamza na cewa makarantun na fadakarwa game da zaman lafiya da fahimtar juna.

XS
SM
MD
LG