Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsofaffin Jakadun Amurka a Kasashen Afrika 78 Sun Nuna Damuwa ga Kalaman Batancin Trump


Shugaban Trump a Fadar White House
Shugaban Trump a Fadar White House

Tsofaffin jakadun Amurka a kasashen Afrika guda saba’in da takwas sun aikawa fadar shugaban Amurka ta White House da wasika, suna bayyana matukar damuwa dangane da kalaman batancin da aka ce shugaba Donald Trump ya yi inda ya kira kasashen Afrika kaskantattu.

Wasikar ta jinjina wa fitattun ‘yan kasuwa, da ‘yan gwaggwarmaya da masu ra’ayin ‘yan mazan jiya da kuma ‘yan boko daga nahiyar suka yi, yayinda kuma suke jadada bukatar a ci gaba da karfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen nahiyar Afrika din da Amurka.

Daya daga cikin wadanda suka sa hannu a wasikar, kuma tsohon jakaden Amurka a Najeriya, John Campbell ya shaidawa Muryar Amurka cewa, an maidawa shugaban kasar martani da kakkausan lafazi kuma korafin karuwa yake yi ba raguwa ba.

Campbell yace ministan harkokin kasashen waje na Najaeriya ya gayyaci jami’an diplomasiya na Amurka domin su yi bayani a kan kalaman na Trump da ya bayyana a masayin masu matukar bakanta rai, da kuma batanci, kuma ba za a lamunta da su ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG