Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Ya Koma Gida


Tsohon gwamnan jihar Isa Yuguda ya is birnin Bauchi

Makada da mawaka suka dinga sheke ayarsu a filin saukan jiragen sama dake garin Bauchi domin tarbar tsohon gwamnan jihar Isa Yuguda wanda ya fice daga jihar bayan da jam'iyyarsa ta sha kaye a zaben 2015

Daruruwan magoya bayansa suka yi dafifi a harabar filin jirin saman domin su ga tsohon gwamnansu.

Wadanda suka je tarbar tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda
Wadanda suka je tarbar tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda

Shi dai tsohon gwamnan ya bar kasar ne kimanin shekaru biyu bayan da jam'iyyarsa ta sha kaye a zaben 2015, da nufin yin jinya a kasar Ingila.

Inji tsohon kwamishanan yada labarai na tsohon gwamnan Alhaji Salisu Barau Tafawa Balewa, gwamnan ya dawo jihar ne domin ya godewa mutanen jihar bayan da ya gama jinya a kasar waje. Tsohon kwamishanan yace ranar dawowar tsohon gwamnan rana ce ta yiwa Allah godiya.

A kan matsayin tsohon gwamnan a siyasa yace a bar maganar sai lokacin siyasa ya zo zai yi tunanen irin rawar da zai taka. Amma yanzu kowa ya dinga yiwa shugaban kasa Muhammad Buhari addu'a.

Da aka tambayeshi ko gaskiya ne hukumar EFCC ta kwace gidan da yake ciki sai yace a je a tambayi hukumar.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

XS
SM
MD
LG