Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Gwamnan Lagos Lateef Jakande Ya Rasu


 Alhaji Lateef Jakonde
Alhaji Lateef Jakonde

Gwamnan farin kaya na farko a jihar Lagos, Lateef Jakande ya rasu yau Alhamis yana da shekaru 91 a duniya.

Lateef Jakande, wanda yake daya daga cikin almajiran tsohon firimiyan yankin kudu maso yammacin Najeriya, Obafemi Awolowo, ya yi mulki a matsayin gwamnan jihar Lagos tsakanin shekarar 1979 zuwa 1983.

Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan Alhaji Lateef Kayode Jakande a shafinsa na Twitter

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya yaba aikin da marigayin ya yi lokacin yana dan jarida, da kuma shugabancin kwarai da marigayin ya yi a matsayin gwamnan jihar Lagos, da gwamnan ya ce zai zama abin koyi ga wadanda za su biyo baya. Ya bayyana rasuwar tsohon gwamnan a matsayin babban rashi ga jihar da kuma kasa baki daya.

Lateef Jakonde da Babajide Sanwo-Olu
Lateef Jakonde da Babajide Sanwo-Olu

Bayan gama wa’adin mulkinsa, marigayin ya kuma yi aiki a matsayin Ministan ayyuka karkashin mulkin soji na janar Sani Abacha. Yana daya daga cikin gwamnonin da ake yaba ayyukan raya jihohinsu a Najeriya, inda a zamanin sa, ya samar da ababan jin dadin rayuwa ga al’ummar jihar Lagos da suka hada da gidaje masu saukin kudi ga talakawa, da kuma yin gagarumin garambawul a fannin ilimi a duk fadin jihar, wanda kawo yanzu, babu gwamnan da ya doke wannan shirin.

Alhaji Lateef Jakande shi ne tsohon gwamnan jihar Lagos na biyu da suka rasu a cikin wannan shekarar. Kafin rasuwarsa, tsohon gwamnan jihar karkashin mulkin soja, Riya Admiral Ndubuisi Kanu ya rasu ranar 14 ga watan Janairu yana da shekaru 77 a duniya.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG