Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Ministan Lafiyar Najeriya Osotimehin Ya Rasu


Marigayi Babatunde Osotimehin (VOA Photo Credit R. Corben)
Marigayi Babatunde Osotimehin (VOA Photo Credit R. Corben)

Tsohon ministan lafiya a Najeriya Prof. Babatunde Osotimehin wanda ke rike da mukamin Hukumar dake sa ido kan yawan al’uma ta UNFPA a Majalisar Dinkin Duniya ya rasu.

Babatunde ya rasu da sanyin safiyar yau Litinin yana mai shekaru 68 kamar yadda jaridun yanar gizo a Najeriya da dama suka ruwaito.

Rahotannin ba su bayyana musabbabin mutuwar tsohon ministan ba wanda ya rike mukamin ministan lafiya a zamanin mulkin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua.

An haifi Mr. Babatunde ne a watan Fabrairun shekarar 1949 kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG