Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Amurka George W.H. Bush Ya Mutu


 George H.W. Bush
George H.W. Bush

Allah ya yiwa George H.W. Bush tsohon shugaban kasar Amurka rasuwa yana da shekaru 94 a duniya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun iyalan gidan Bush ya fitar, na cewa da George Bush ya mutu ne da yammacin jiya Juma’a.

George H.W. Bush shi ne shugaban Amurka na 41 kuma tsohon shugaban kasar mafi dadewa a raye, ya yi shugabancin ne tsakanin 1989 da 1993.

Ranar 17 ga watan Afrilun wannan shekarar ne uwargidansa Barbara Bush ta mutu tana da shekaru 92 a duniya.

George Bush dai ya yi fama da rashin lafiya inda a kwanakin baya bayan mutuwar matarsa aka kwantar da shi a asibiti, bayan kamuwa da wata cuta da ta yadu a jininsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG