Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Madeliene Albright Ta Rasu


Tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka Madeleine Albright, ranar 10 ga watan Janairu, 2017.

Albright ta rasu ne bayan fama da cutar kansa kamar yadda iyalanta suka sanar a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka, kuma mace ta farko da ta rike wannan mukami, Madeleine Albright ta rasu. Shekarunta 84.

Albright ta rasu ne bayan fama da cutar kansa kamar yadda iyalanta suka sanar a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

“Ta kasance zagaye da iyalanta da abokanai,” iyalanta suka ce a wani sakon Twitter da suka wallafa.

“Mun yi rashin uwa, kaka, ‘yar uwa, gwaggo da kawa.” Sakon ya kara da cewa.

A shekarar 1996 tsohon shugaban Amurka Bill Clinton, ya nada Albright a wannan mukami, inda ta rike mukamin tsawon shekaru hudu na karshen wa’adin mulkinsa.

A baya ta taba rike mukamin jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya duk a karkashin zamanin mulkin Clinton.

A wancan lokaci, ita ce mace da ke rike da mukami mafi girma a tarihin gwamnatin Amurka.

Ko da yake, duk da kwarewarta a fannin siyasa da harkokin diflomasiyya, Albright ba ta shiga sahun wadanda za su iya neman mukamin shugaban Amurka ba , saboda asalinta daga birnin Prague na kasar Czech take.

A shekarar 2012, tsohon shugaban Amurka, Barack Obama ya karrama ta da lambar yabo ta “Medal of Freedom,” wacce ita ce mafi girma a kasar.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG