Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tunawa Da Whitney Houston


Tunawa Da Whitney Houston

Shahararriyar mawakiyar mai shekaru 48 da haihuwa, ta lashe lambobin yabo har 415 kafin rasuwarta ran asabar.

An bayar da sanarwar mutuwar shahararriyar mawakiyar nan, Whitney Houston.

Whitney Elizabeth Houston, mai shekaru 48 da haihuwa, ta rasu ranar asabar.

A shekara ta 2009, Kundin Tarihi na Duniya mai suna "Guiness Book of World Records" ya bayyana Whitney Houston a zaman mace mawakiya da ta fi kowa samun kyautar lambobin yabo, inda ta samu lambobi 415 a rayuwarta.

Cikin lambobin yabon nata har da Lambar Yabon Waka ta Grammy guda 6, da lmbar yabon Waka ta Billboard guda 30, da lambar yabon Waka ta American Music Award guda 22, da kuma lambar yabon Emmy guda 2 a saboda rawar da ta taka a matsayin jaruma cikin fina-finai.

Filinb "A Bari ya Huce..." na ranar asabar mai zuwa zai waiwayi rayuwar marigayiya Whitney Houston.

XS
SM
MD
LG