Accessibility links

An yi bukin tunawa da rayuwar mawakiya Whitney Houston


Whitney Houston

Masana'antar tallata kade kade ta Amurka ta karrama marigayiya Whitney Houston

Kamfanonin tallata kade kade na Amurka sun yi bukin tunawa da rayuwar fitattar mawakiyar nan da ‘yar wasa funa funai da ta sami lambonin yabon Grammy Whitney Houston a otel din dake birnin Los Angeles inda aka same ta matatta jiya.

Malamin Houston babban abokinta da kuma mai harhada wakokinta, Clive Davis ya fadi tarihinta jiya da dare a wajen bukin wake waken da ya shirya a otel din Beverly Hilton.

Davis da ya yi magana da nauyin zuciya yce,, “Whitney zata so a ci gaba da kade kaden, danginta kuma sun ce mu ci gaba” Dukan mawakan da suka yi waka sun yi jawaban karrama Houston.

Yan sanda sun ce an sanar da mutuwar Houston ne jiya da yamma bayan da aka same ta matatta a dakinta dake hawa hutu na otel din Beverly Hilton.

Kakakin ‘yan sandan Beverly Hills Mark Rosen yace jami’an yan sanda da kuma ma’aikatan jinya sun isa dakin Houston cikin mintoci kalilan bayanda suka sami kira cewa ana bukatar taimakon gaggawa.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG