Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya Ta Sake Wani Faston Amurka Bayan Ta Daure Shi Shekaru Biyu


Pastor Andrew Brunson, saye da farar riga
Pastor Andrew Brunson, saye da farar riga

Wata kotun Turkiya ta saki wani ba-Amurke fasto, Andrew Brunson, lamarin da ya kawo karshen tankiyar diflomasiya tsakanin Washington da Ankara.

Brunson yana huskantar shari’ar da zata iya daure tsawon shekaru 35 idan har an same shi da aikata laifin ta’addanci da kuma leken asiri, zargin da Amurka ta kira mara tushe.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa manema labarai cewa Brunson, ya sha wahala sosai, amma yanzu dai wahalar ta kare kuma zai kawo ziyara a fadar White House nan bada dadewa ba. A wani sakon Twitter da ya aike, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace gwamnatin zata ci da da yin aiki wurin kwato Amurkawan da aka dauresu bisa kuskure zuwa gida.

Jirgin saman sojojin Amurka ne zai dauko Brunson zuwa filin saukar jiragen soji na Ramstein a kasar Jamus inda za a duba lafiyarsa, kana daga bisani a karaso da shi zuwa Amurka a yau Asabar. Shugaba Trump ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar Brunson zai iso nan Washington kuma ya kawo ziyara a fadar White House a yau Asabar.

A jiya Juma’a ne kotun Turkiyar ta same shi da laifi, amma kuma sai ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru uku da wata daya. Tuni da shi wannan faston ya kwashe shekaru biyu yana zaman gidan yari yayin da ake shari’ar, lamarin da ya kai ga sake shi saboda lokacin da ya kwashe a gidan kason.

A ranar Alhamis ne wasu kafafen labarai a nan Amurka suka ce Washington da Ankara sun yi wata ganawar fahimtar juna a kan wannan batu kuma hakan zai sa a sako Brunson.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG