Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Na Zargin Malaminsu Mazaunin Amurka Da Hannu a Yunkurin Juyin Mulki


Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Tare Da Malaminsu Mazaunin Amurka Da Suke Zargi Da Hannu a Yunkurin Juying Mulki
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan Tare Da Malaminsu Mazaunin Amurka Da Suke Zargi Da Hannu a Yunkurin Juying Mulki

Jami’an Turkiyya sun ce an kama wasu daga cikin sojoji 2,839 da suka hada da manyan hafsoshi, wadanda suka yi yunkurin kifar da gwamnati a shekaran jiya Juma’a.

Haka an bada rahoton dakatar da alkalai kusan 2,745 bisa zargin alaka da wani Malamin addini Fetullah Gulen. Kafar yada labaran Turkiyya tace an mika sammaci 140 ga wasu ma’aikatan babbar kotun kasar.

Malamin da aka zarga da hannu a wannan yunkuri Fetullah, wanda yake zaune a jihar Pennsylvania ta nan Amurka, ya nisanta kansa da yunkurin juyin mulkin.

Sakataren harkokin wajen Amurka yace, Turkiyya bata bukace su da mika Shehin Malamin ba, to amma Amurka a shirye take ta mika shi matukar aka sami kwararan hujjojin cewa yana da hannu a yunkurin juyin mulkin da ya kasa kaiwa ga gaci.

Har yanzu dai ba wanda ke da yakinin ko suwa ke rike da ikon shelkwatar sojin kasar ta Turkiyya. Firayimistan kasar Binali Yildrim ya yiwa jama’a jawabi a yau Asabar game da yunkiurin juyin mulkin da aka yi, yace, wannan bakin tabo ga kasarsu.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG