Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Tura Sojojin Haya Zuwa Libya


Libya War
Libya War

Majiyoyi a kasashen Libya da Somalia sun ce Turkiya ta tura sojojin haya zuwa Libya daga Somalia domin su fafata da sojojin gabashin Libya karkashin jagorancin kwamanda Khalifa Haftar.

Darektan ayyukan jarida na sojin Libya kanal Khaled Mahjoub ya fadawa gidan talbiji na Larabawa a makon da ya gabata cewa, Turkiya ta aike da dubban sojojin haya su yi yaki tare da wata kungiyar ‘yan bindiga da ke Libya domin su kwace ikon garin Sirte mai muhimmanci.

Sai dai ba iya gano ko an tura sojojin hayar Somalia ne su shiga sawun gaba ba.

Gwamnatin yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, karkashin jagorancin Firai Minista Fayez al-Sarraj, ta lashi takobin sake kwato birnin mai tashar jirgin ruwa daga rundunar LNA ta Khalifa Haftar.

A gefe guda kuma, shafin yanar gizo na Somali Guardian ta bada rahoto a karshen mako cewa baicin Turkiya da Qatar da suka jibge ko kuma suna niyar jibge dubun dubatar mayaka a Libya, wasu a ciki an dauke su ne su yi aiki a matsayin sojojin Qatar.

An kafe hotuna da bidiyon mutanen da ake zaton sojojin haya ne a kan shafukan yanar gizo na kafafen labaran Larabawa da dama.

Turkiya ta kafa shingayen sojoji da dama a Somalia. Turkiya da Qatar sun horar da sojojin Somalia da jami’an tattara bayanan sirii a cewa kafar yada labaran Larabawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG