Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Twitter A Ghana: Mu Muka Dabawa Kanmu Wuka - Lai Mohammed


Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Muhammad yayin wani taron Majalisar zartaswa
Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Muhammad yayin wani taron Majalisar zartaswa

Amma ministan ya ce, kamata ya yi Twitter ya zabi Najeriya, lura da cewa mutum miliyan 25 suke amfani da shafin a Najeriya, abin da ya dara mutum miliyan 8 da Ghana take da shi.

Ministan yada labarai a Najeriya, Lai Mohamed, ya dora alhakin ajiye Najeriya da kamfanin Twitter ya yi a gefe ya zabi Ghana a matsayin kasar da zai bude reshensa a nahiyar Afirka.

A ranar Litinin din makon da ya gabata, Twitter ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa zai bude reshensa a na nahiyar Afirka a kasar Ghana.

Hakan ya janyo suka daga ‘yan Najeriya da dama, wadanda suka yi ta inkarin cewa adadin mutanen da ke amfani da Twitter a kasar, ya fi yawan al’umar kasar Ghana baki daya.

Jama’a da dama a kasar sun yi korafin cewa Najeriya ce ta cancanci wannan matsayi lura da cewa ita ta fi kowacce kasa karfin tattalin arziki a nahiyar.

Sai dai a wani martani da ya mayar yayin da yake ganawa manema labarai a Abuja a karshen makon da ya gabata, Mohammed ya ce rashin kishin kasa da ‘yan Najeriya suke nunawa, shi ya sa kamfanin na Twitter ya tsallake kasar ya zabi makwabciyarta ta Ghana.

“Abin da muka shuka shi muka girba,” in ji Mohamed, wanda ya ce yadda kafafen yada labaran kasar suke shafawa kasar bakin fenti a irin rahotanninsu, shi ya haifar da abin da aka gani.

Jack Dorsey, wanda ya mallaki Twitter
Jack Dorsey, wanda ya mallaki Twitter

Amma ministan ya ce, kamata ya yi Twitter ya zabi Najeriya, lura da cewa mutum miliyan 25 suke amfani da shafin a Najeriya, abin da ya dara mutum miliyan 8 da Ghana take da shi, kamar yadda Channels TV ya ruwaito ministan.

Kamfanin NOI da ke kiddiga kan kafafen sada zumunta, ya ce mutum miliyan 39 ne ke amfani da Twitter a Najeriya, adadin da ya haura al’umar kasar ta Ghana mai mutum miliyan 36.

A sanarwar da ya fitar a makon jiya, kamfanin na Twitter ya yaba da wasu batutuwa da ya ce ya lura da su a kasar ta Ghana, dalili kenan da ya sa zabi kasar.

“Ghana kasa ce mai dabbaka tsarin dimokradiyya, mai kare fadin albarkacin baki, da tabbatar da walwala a yanar gizo, wadanda kuma duk abubuwa ne da kamfanin Twitter yake adabbakawa.” Twitter ya ce.

XS
SM
MD
LG