Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UEFA: Chelsea Ta Yi Kunnen Doki Da Madrid A Spain


Chelsea
Chelsea

Chelsea ta fara saita kanta akan layin kokarin lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA bayan da ta bi Real Madrid gida ta yi kunnen doki da ita.

An tashi a wasan na semi-final ne da ci 1-1, wanda aka buga a Estadio Alfredo Di Stefano.

Dan wasan Chelsea Pulisic ne ya fara zura kwallo a minti na 14, sai Karim Benzama ya farke kwallon a minti na 29.

Duk da cewa Chelsea ta fi taka kwallo a wasan, musamman kafin a je hutun rabin lokaci, wasan wanda aka kare shi a cikin ruwa sharkaf, bai ba ta damar tafiya gida da makinta uku ba.

Kalubalen da ke gaban Madrid shi ne, sai ta lashe wasan zagaye na biyu da za a yi a Stamford Bridge a London nan da kwana bakwai.

Ita kuwa Chelsea, ta fara jin kamshin karawa da Manchester City ko Paris Saint Germain a wasan karshe da za a yi a ranar 27 ga watan Mayun 2021 a birnin Santanbul na kasar Turkiyya.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, kusan babu wani abu da ya sauya a wasan, yayin da duka bangarorin biyu suka yi ta kokarin kare kansu daga shammatar abokin hamayya.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG