Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

UEFA Da FIFA Ba Sa Kyautawa ‘Yan Wasa - Pep Guadiola


UEFA Da FIFA Ba Sa Kyautawa ‘Yan Wasa - Pep Guadiola
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00

Pep Guradiola ya caccaki hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA saboda rashin hutun da ba sa ba ‘yan wasa. Yanzu haka Manchester City na kokarin ganin ta lashe gasa hudu a wannan kakar wasa ta bana. A cewar manajan kungiyar ta City, ‘yan wasansa mutane ne ba na’urori ba.

Pep Guardiola ya caccaki hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA saboda rashin hutun da ba sa ba ‘yan wasa.

Yanzu haka Manchester City na kokarin ganin ta lashe gasa hudu a wannan kakar wasa ta bana. A cewar manajan kungiyar ta City, ‘yan wasansa mutane ne ba na’urori ba.

“UEFA da FIFA suna nakasa ‘yan wasa saboda abin ya yi yawa.” – Pep Guardiola ya ce.

Karin bayani akan: Pep Guardiola​, Manchester City, FIFA, UEFA, da Premier League.

Manajan na City ya kara da cewa, kungiyarsa ba ta samu hutun tsakiyar mako ko da so daya ba a wannan kakar wasa, saboda barkewar annobar COVID-19, hakazalika, ita ma hukumar UEFA, haka ta jero wasanninta amma kuma ta takaita tazarar da ke tsakaninsu.

Akan dai ba da tazarar makonnin ne a wasanin zagaye da ake bugawa a wannan kakar wasa yayin da a bara akan buga su ne cikin wata uku.

XS
SM
MD
LG