Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

YUGANDA: Ma'aikatar Lafiya Ta Tabbatar Da Barkewar Cutar Shan Inna


Ma'aikatar lafiya ta Uganda ta tabbatar da barkewar cutar shan inna a cikin kasar bayan samfuran da aka tattara daga ruwan najasa a Bugolobi da Lubigi.

Ma'aikatar ta ce gwaje -gwajen sun tabbatar da wani nau'in kwayar cutar mai kamuwa da cutar Shan inna. Ma'aikatar ta ce za a iya alakanta sake bullar cutar shan inna a Uganda saboda rage allurar rigakafin cutar shan inna a Uganda yayin barkewar cutar ta Covid-19 da kuma tsallaken iyaka tsakanin kasashe makwabta.

Emmanuel Ainebyoona babban jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta Uganda ya shaidawa wakilin Muryar Amurka James Butty cewa ma’aikatar ta kara sa ido kan cutar shan inna kuma za ta gudanar da allurar rigakafin cutar shan inna a cikin watan Oktoba da Disamba na wannan shekarar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana Uganda da yawancin Afirka a cikin 2020 a matsayin kasashen da suka shawo kan cutar shan inna.

Sai dai, Ainebyoona ya ce an sake samun bulowar cutar shan inna da wani nau'in wanda ke shafar yara a cikin al'ummomin da ke da ƙarancin kariyar lafiyar jiki.


XS
SM
MD
LG