Accessibility links

Ukraine: Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kiran Mutunta Yarjejeniya


FILE - United Nations Secretary-General Ban Ki-moon, Apr. 28, 2015.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin dake takaddama da juna a kasar Ukraine da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon shekarar nan.

Majalisar Dinkin Duniyan ta fitar da wannan sanarwar ne yayin da wani babban jami’in tsaron gwamnatin Amurka da wasu jami’an diplomasiyya ke shirin ganawa a yau juma’a a Jamus.

Rahotanni sun ce tattaunawar wadda ta duba karfin takunkuman da aka kakabawa Rasha da kuma matakan da kungiyar tsaro ta NATO ke dauka wajen jan kunnen kasar Rasha.

A lokacin gudanar da taron, mataimakin kungiyar hadin kan kasashen turai da saka ido kan rikicin na Ukraine, ya gayawa taron ta kafar sadarwar bidiyo cewa an girke muggan makamai a inda yarjejeniyar tsagaitar wuta ta haramta yin hakan.

Ambasadan kasar Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya, Yuriy Sergeyev, ya zargi Rasha da masu mara mata baya a gabashin Ukraine da saba yarjejeniyar tsagaita wutar.

Rasha dai ta jima tana musanta zargin da ake mata na sa hanu a rikicin na Ukraine.

XS
SM
MD
LG