Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohi 2 Kacal Suka Rage Kafin Sanin Makomar Zaben Afirka Ta Kudu


Zaben Afirka Ta Kudu
Zaben Afirka Ta Kudu

Jihohi biyu suka rage ace an kai ga kammala kidayar kuri’u da kaso 99 daga cikin 100 na zaben da aka gudanar a Afirka ta Kudu. Zaben da jam’iyyar ANC mai mai mulki ke ta shan kashi bisa ga kidayar kuri’un.

Har yanzu ana ta harhado kan lissafin kuri’un a manyan jihohin da jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ke shinshino nasara. Jihohin kamar Johannesburg jiha mafi girma kuma cibiyar kasuwancin kasar.

Sai kuma Pretoria da take a matsayin babban birnin kasar. Sai dai har yanzu, jami’iyyar ANC ta su Marigayi Shugaba Nelson Mandela, ita ke kan gaba da kaso 53 na kuri’un da aka kidaya zuwa yanzu.

Mai fashin baki SomaDoda Fikeni ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, koma bayan da ANC ta gani a zaben kasar, yana da nasaba da yadda ‘yan kasar suke kule da jam’iyyar ne game da matsalar rashin aikin yi da rashawa a siyasar kasar.

XS
SM
MD
LG