Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa'adin Korar Fulani Daga Dazukan Jihar Delta Na Ci Gaba Da Janyo Ce-ce-ku-ce


Hukumomin 'yan sanda da gwamnati a jihar Delta da ke Kudancin Najeriya sun ce sam ba su da masaniya akan wa'adin da shugaban karamar hukumar Oshimili ta Arewa ya baiwa Fulani makiyaya da su fice daga yankin.

Wa'adin mako daya da majalisar karamar hukumar Oshimili North a jihar Delta, ta baiwa Fulani makiyaya su bar dazukan karamar hukumar na ci gaba da haddasa ce-ce-ku-ce daga sassa daban-daban na Najeriya.

A ranar litinin din da ta gabata shugaban karamar hukumar Mista Louis Ndukwe ya shaida manema labarai cewa, yawan garkuwa da mutane da yawan kashe-kashe da kuma wasu ayyukan assha da suka addabi al’ummar yankin ne suka sa aka dauki wannan matakin, kuma ya bayar da umarnin ne tare da amincewar hukuma da Sarakuna gargajiya da duk masu ruwa da tsaki a karamar Hukumar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Delta Malam Hafiz Muhammad Inuwa ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, su ba su da masaniya akan wannan umarnin da Mista Louis Ndukwe ya ce ya bayar, kuma hukumar ‘yan sanda baza ta yarda da duk abinda ba ya bisa doka ko kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sakataren kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah reshen jihar, Mallam Muktar Usman ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, gwamnan jihar ya shaida musu cewa bai san da wannan umarnin ba, kuma suna iya kokarin su tare da hadin guiwar hukumomi da gwamnati don ganin an fitar da bata gari da kuma kawo daidaito da zaman lafiya.

Saurari Karin bayani cikin. Sauti daga Alphonsus Okoroigwe.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG