Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa Ya Kashe Alex Badeh?


Marigayi Alex S. Badeh a wani hoto da aka dauka a watan Janairun, 20, 2014.

An kashe Badeh ne akan hanyar Abuja zuwa keffi yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga gonarsa kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wasun ‘ýan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun harbe babban tsohon hafsan tsaron Najeriya Alex Badeh.

An kashe Badeh ne akan hanyar Abuja zuwa keffi yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga gonarsa kamar yadda rahotanni suka nuna.

Rundunar sojin saman Najeriya ta tabbatar da mutuwar tsohon babban hafsan tsaron na Najeriya.

“A madadin dakarun saman Najeriya maza da mata, shugaban dakarun saman Najeriya, Air Marshal Abubakar, na mika sakon taáziyya ga iyalan babban tsohon hafsan tsaron Najeriya, bisa wannan babban rashi, muna fatan Allah ya jikan sa,” kamar yadda Kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commadore Ibukunle Daramola, ya wallafa a shafin Twitter na rundunar.

A shekarun baya, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, ta tuhumi Badeh da yin sama da fadi da wasu makudan kudade a lokacin yana ofis, lamarin da ya sa take tuhumar shi.

Kisan Alex Badeh-3;30"
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Wannan kisa na faruwa ne kasa da watanni uku, bayan da aka kashe tsohon shugaban gudanarwa na rundunar sojin Najeriya, Major General Idris Alkali, wanda ya bata a ranar 3 ga watan Satumba.

Amma an gano gawarsa a cikin wata rijiya, bayan da aka kama wasu gungun mutane da ake zargi da kisan a yankin Dura Du na karamar hukumar Jos ta Kudu da ke jihar Pilato.

Marigayi General Alkali, na kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja a lokacin da aka tsare shi aka mai kisan gilla.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG