Accessibility links

Wadanda suka mutu a girgizar kasar Himalaya sun kai 100

  • Ibrahim Garba

Irin yadda hanyoyi su ka lalace sanadiyyar girgizar kasa.

Masu ayyukan ceto na ta fama da lalatattun hanyoyi da gocewar kasa

Masu ayyukan ceto na ta fama da lalatattun hanyoyi da gocewar kasa a wurare da dama a kokarinsu na kaiwa ga wuraren da gigizar kasar Himalaya da ta kashe mutane 100 ta shafa.

Girgizar kasar mai karfin 6.9 a ma’aunin girgizar kasa ta fi karfi ne a jihar Sikkim ta Indiya ta haddasa barna da mace-mace a fadin arewa maso gabashin Indiya, da Nepal da kuma yankin Tibet na China.

Hukumomin Sikkim sun fadi yau Laraba cewa har yanzu ba a jin duriyar wasu kauyukan da ke sashen da girgizar kasar ta shafa, don haka adadin wadanda su ka mutu na iya karuwa.

Wani kamfanin da ke gina tashar samar da wutar lantarki a rewacin Sikkim y ace akalla ma’aikatasa 17 sun mutu sanadiyyar gocewar kasar da girgizar kasar ta haddasa. Har yanzu ba a san inda wasu ma’aikata da dama su ke ba.

Jami’an sojoji sun ce akalla masu yawon bude ido 45, ciki hard a wasu ‘yan kasashen waje da dama, sun sami kubuta da taimakon wani jirgi mai saukar ungulu a yau Laraba, bayan sun makale a sanannen tudun yawon shakatawa na Lachung.

Hukumomi a Nepal sun bayar da labarin mace-mace har guda 7 da ked a nasaba da girgizar kasar, a sa’ilinda kuma kamfanin dillancin labaran gwamnatin China na Zinhua y ace akalla mutane 7 sun mutu a kudancin Tibet.

Wasu mutanen 8 kuma sun hallaka a jihohin Yammacin Bengal da Bihar na kasar Indiya.

Yawan gocewar kasa, da hazo da kuma ruwan sama mai yawa, sun hana ma’aikatan ceto da dama isa wuraren da abin ya fi muni. An shiga ayyukan ceto gadan-gadan a yaub Laraba, bayan da sojoji sama da 5,000 su ka bararraka duwatsun da su ka fada kan babbar hanyar da ke kaiwa Mangan, wanda gari ne da ke kusa da inda girgizar kasar ta fara.

XS
SM
MD
LG