Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilan kwamatin sulhun MDD su 15 sun amince da kudurin Rasha na jaddada hana makamai masu linzamin Libya fadawa hannun ‘yan tawaye


Litinin da ta gabata ce Majalisar Gwamnatin riko a Libya ta zabi shehin Malamin birnin Tripoli al-Keeb domin zama sabon friministan kasar Libya ke yiwa taron manema labarai jawabi.

Kwamatin sulhun MDD yayi kira ga hukmomin kasar Libya das u dauki matakan hana bazuwar Makamai masu linzami zuwa yankunan dake Makwabtaka da Libya. Kwamatin sulhun yayi wnanan kiran ne a dai dai lokacin da hukumomin wucin gadi kasar suka zabo sabon friministan wucin gadi wanda zai yi jagorancin shirin sauyin siyasr da ake yi a kasar Libya.

Gefe guda kuma, Majalisar Mulkin Wucin gadi ta kasar Libya ta zabi Abdel Rahim el-Keeb a matsayin sabon friministan wucin gadi. Litinin da ta gabata ce ‘yan majalisar mulkin wucin gadin suka suka zabi El-Keeb da kuri’u 26 daga cikin 51. El-Keeb injiniyan lantarki ne wanda yayi karatu a a Amurka, kuma shine zai yi jagorancin kafa sabuwar Gwamnati a Libya har zuwa lokacin gudanar da sabon zabe.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG