Accessibility links

Amirka zata tura jiragen yakin da babu matuka a ciki zuwa Somaliya

  • Jummai Ali

Sojojin Kenya ne ke gadi, a wani wuri da bam ya tashi.

Amirka ta tabatar cewa zata tura jiragen saman yakinta wadanda na'ura ke sarafawa, wadanda ke kasar Ethiopia zuwa Somaliya domin gudanar da bincike.

Amirka ta tabbatar cewa zata tura jiragen saman yaki, wadanda na'ura ke sarrafawa, wadanda yanzu hak suke kasar Ethiopia zuwa Somaliya domin gudanar da aiyukan bincike.

Jami'an Amirka sunce jiragen saman yakin da babu matuka a ciki, zasu tashi ne daga wani filin saukar jiragen sama a birnin Arba Minch dake kudanci kasar Ethiopia zuwa Somaliya inda gwamnati ke fafatawa da kungiyar yan yakin sa kai ta Al Shabab wadda take da alaka da kungiyar Al Qaida.

Ana iya dankarawa irin wadannan jiragen saman yaki makamai masu linzami da bama bamai da watann dan adama ke harba su, to amma mai magana da yawu rundunar sojan Amirka Cammandan mayakan ruwa James Stockman ya fadawa Muryar Amirka a yau juma'a cewa, jiragen zasu gudanar da shawagin bincike ne kurum.

Haka kuma Kwamanda Stockman yace, aiyukan da jiragen zasu gudanar basu da alaka da hare haren da sojojin Kemya ke kaiwa cikin Somaliya a yanzu.

Yace Amirka bata da sansanonin soja a Afrika in baicin a kasar Djibouti, kuma jami'an sojan Amirka kalilan ne suke aiki a Ethiopia.

Makoni biyu da suka shige sojojin Kenya suka kutsa Somaliya domin farautar yan yakin sa kai, wadanda kasar kenya ta ke tsamani cewa, sune keda alhakin sace mutane daga yankunan Kenyan.

A yau juma'a sojojin Kenya dana Somaliya suka kwace birnin Burgabo dake yankin Juba. Yanzu haka kuma sojojin Kenya suna tazarar kilimota maitan daga birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa, birnin na uku wajen girma a Somaliya.

XS
SM
MD
LG