Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana tattaunawa da dan tsohon shugaban kasar Libya da nufin neman ya yi saranda


Seif al-Islam Gadhafi

Ana tattaunawa ta bayan fage tsakanin dan tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi da ake nema ruwa a jallo da kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa-ICC.

Ana tattaunawa ta bayan fage tsakanin dan tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi da ake nema ruwa a jallo da kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa-ICC.

Ana tuhumar Seif al-Islam Gadhafi da keta hadin bil’adama ta wajen kashe farin kaya dake zanga zanga yayin tarzomar kin jinin mulkin mahaifinshi.

Babban mai shigar da kara na kotun bin kadin laifuka da ta kasa da kasa Luis Moreno-Ocampo yace masu shiga tsakani sun tuntubi Seif al-Islam Gadhafi domin tabbatar da ganin an yi mashi shari’ar adalci. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci ta bakin mai shigar da karar yau asabar cewa, Seif al-Islam ya shaidawa masu shiga tsakanin cewa bai aikata laifukan da ake tuhumarshi a kai ba.

Ana kyautata zaton Seif al-Islam yana kan hanyarshi zuwa wata kasar Afrika dake makwabtaka da Libya ta cikin Hamada.

A halin da ake ciki kuma kungiyar tsaro ta NATO ta bayyana shirin nada I nata I nata ta fice daga Libya ranar Litinin, bayan kai farmakin sararin sama na tsawon watanni bakwai. Ministocin kungiyar ne suka tsaida shawarar janyewa daga Libya jiya jumma’a wanda zai kawo karshen hare haren da kungiyar ta rika kaiwa ta sararin sama. Babban kwamandan kungiyar kawancen tsaron ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya bayyana cewa, kungiyar ta kamala aikinta zata kuma janye cikin tsanaki.

Kungiyar ta sanar da wannan matsayin ne bayanda kwamitin Sulhu na MDD ya kada kuri’ar soke izinin ya bada damar kai wannan samammen.

XS
SM
MD
LG