Accessibility links

Wanda ake zargi da harbe-harbe a wata Jami'a a California, ya kuhula ne saboda korarsa da aka yi

  • Ibrahim Garba

Jami'an tsaro na bincike a harabar makarantar.

‘Yan sanda a birnin Oakland na jihar California, sun ce tsohon dan makarantan

‘Yan sanda a birnin Oakland na jihar California, sun ce tsohon dan makarantan nan da ya kashe mutane 7 jiya Litini a wani kwalejin Kirista da akasari Koriyawan da ke Amurka ne ke tafiya, ya kuhula ne saboda korarsa da hukumar makarantar ta yi a farkon wannan shekarar.

Shugaban Hukumar ‘yan sandan Oakland Jordan Howard ya gaya wa kafar yada labaran CNN a yau Talata cewa One L. Goh, wanda haifaffen dan Koriya ta Kudu ne, ya shiga Jami’ar ta Goh da nufin daukar fansa musamman kan wata jami’ar hukumar makarantar.

Da shigarsa, a cewar Jordan, sai Goh ya yi garkuwa da wata mai karbar baki sannan ya shiga wani aji, inda ya umurci wasu su tsaya jikin bango ya yi ta harbinsu daya bayan daya. Baya ga wadanda su ka mutu, wasu guda 3 sun sami raunuka.

Jordan ya bayyana al’amarin da cewa na fitar hankali ne. Ya ce harbin da ya faru a ajin wani shiryayyen kisan gilla ne.

XS
SM
MD
LG