Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wane Ne Sabon Kocin Super Eagles Jose Peseiro?


Sabon kocin Super Eagles Jose Peseiro
Sabon kocin Super Eagles Jose Peseiro

Peseiro ya taba rike mukamin mataimakin koci a kungiyar Real Madrid a tsakanin shekarun 2003-2004

A ranar Laraba hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF ta sanar da Jose Vitor dos Santos Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles.

Nada Peseiro a matsayin sabon kocin tawagar ‘yan wasan na Najeriya na zuwa ne sama da makonni biyu bayan da aka sallami Gernot Rohr.

Bayan sallamar Rohr hukumar kwallon kafar ta NFF ta nada Augustine Eguavoen a matsayin kocin wucin gadi.

An haifi Peseiro a ranar 4 ga watan Afrilun 1960 a garin Coruche da ke kasar Portugal.

A zamanin da yake buga kwallonsa, Peseiro ya kasance dan wasan gaba a tawagar ‘yan wasan kasarsa ta Portugal.

Ya kuma horar da kungiyoyin kwallon kafa da dama ciki har da Sporting CP wacce ya kai gasar UEFA a shekarar 2005.

Dan shekara 61, Peseiro ya kuma horar da ‘yan wasan Venezuela, Sporting Lisbon, FC Porto da kungiyar Al Ahly ta kasar Masar.

‘Yan wasan Venezuela, su ne tawagar da ya horar ta karshe kafin NFF ta dauke shi aiki.

Kazalika Peseiro ya taba zama mataimakin koci a kungiyar Real Madrid a tsakanin shekarun 2003-2004.

Wata sanarwar bayan taro da hukumar ta NFF ta fitar ta nuna cewa Peseiro zai karbi raganar tafiyar da ‘yan wasan na Super Eagle ne bayan an kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON da za a fara a Kamaru.

A ranar 9 ga watan Janairun shekara mai kamawa za a fara gasar ta AFCON za kuma a kammala a ranar 6 ga watan Fabrairun 2022.

Augustine Eguavoen da aka ba rikon kwarya ne zai kai tawagar ‘yan wasan ta Super Eagle gasar, ko da yake, shi ma Peseiro zai halarci gasar, amma zai je ne a matsayin mai sa ido kamar yadda NFF ta ce.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG