Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NFF Ba Ta Min Adalci Ba Da Ta Sallame Ni – Gernot Rohr


Tsohon kocin Super Eagles Gernot Rohr a shekarar 2017.

A cewar Rohr, bai kamata a ce hukumar ta NFF ta dauki wannan mataki gab da za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ba.

Tsohon kocin Super Eagles Gernot Rohr ya ce hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF ba ta yi masa adalci da ta kore shi ba, yana mai cewa kungiyar na taka rawar a zo a gani karkashin jagorancinsa.

A farkon makon nan hukumar ta NFF ta sallami Rohr ta maye gurbinsa da tsohon kyaftin din Super Eagles Augustine Eguaveon.

Sai dai a wata hira da ya yi da ESPN, Rohr ya nuna rashin jin dadinsa dangane da matakin sallamar shi da aka yi, inda ya ce ya cika duka burukan da aka gindaya masa wajen ciyar da kungiyar gaba.

A shekarar 2016 aka nada Rohr a matsayin kocin Super Eagles, shi ne kuma kocin da ya fi dadewa a wannan mukami.

A cewar Rohr, bai kamata a ce hukumar ta NFF ta dauki wannan mataki gab da za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ba.

Ya kara da cewa kungiyar ta Super Eagles ta samu damar da za ta ci karin kwallaye a wasannin da ta buga Saliyo da Cape Verde, amma ba ta yi sa’a ba.

Rohr ya kara da cewa, tun da ya karbi ragamr horar da ‘yan wasan, kungiyar ta kara bunkasa har ta samu karin matsayi a jerin kasashen da suka fi iya taka kwallo a duniya da FIFA ke fitarwa.

Ita dai hukumar ta NFF ba ta fadi takamaiman dalilin sallamar Rohr ba, amma ta mika godiyarta bisa rawar da ya taka wajen inganta wasan kungiyar.

“Hulda tsakanin hukumar NFF ta Najeriya da Mr Rohr ta zo karshe. Muna mika godiyarmu a gare shi bisa ayyukan da ya yi wa Super Eagles da Najeriya.” Babban Sakatare janar na NFF Dr. Mohammed Sanusi ya ce cikin wata sanarwa.

AFCON 2021, Super Eagles

Yan wasan Najeriya na atisaye gabanin karawar da za su yi da Guinea-Bissau a rukunkin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021: Troost-Ekong

Kowa ya san cewa mun iya taka leda’ In ji Troost-Ekong, yayin da Najeriya ta kai zagayen knockouts
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:03 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG