Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Babban Malami Ya Tsallake Rijiya da Baya A Bangladesh


'Yansanda a wurin da 'yan ta'adan suka tada bam

Wani babban malami da ya bada fatwa a kasar Bangledesh yana ALLAH waddarai da kashe mutanen da akayi a kasar kwanan nan, yana cewa duk wanda yayi hakan ya sabawa koyarwan addinin Musulunci shima ya tsallake rijiya da baya,bayan sun kashe wasu wasu mutane 4.

‘Yan mintoci kadan kafin malamin mai suna Fariduddin Masoud ya iso inda zai jagoranci sallar idi a Kishoregash a jiya Alhamis domin bikin sallah karama, ‘yan sanda suka yi arangama da wasu gungun mutane dauke da makamai sun dunfari inda malamin yake, wanda aka ce wata kila sune gungun mutanen da suka yanka wasu ‘yan kasar waje harma da ‘yan kasar ta Banglesdesh a satin da Ya shige a babban birnin kasar wato Dhaka.

Tun farko sai da ‘yan sanda a wani shinge suka kalubalanci wata tawagar mutane dake dauke da bom, da bindigogi da adduna kuma aka ga sun dunfari inda mutane sama da dubu dari ukku suka taru domin gabatar da sallar idi.

Wadanda suke juyayin harin da aka kai
Wadanda suke juyayin harin da aka kai

Fada dai ya fara kaurewa tsakanin wadannan mutanen da ‘yan sanda a wajen filin Kishoregang a filin sallar idi, rahottani sun tabbatar cewa ‘yan taadan sun jefa wa ‘yan sanda bom, wanda ya kashe biyu daga cikin su da mutum guda cikin ‘yan ta'addan sai kuma wata mace da take daga gefen da abin ya faru, sai dai mutane da dama sunji rauni sakamakon bom din da suka tayar, sai dai daya daga cikin maharani wani saurayi dan shekaru 19 ya samu rauni kuma an kame shi da rai.

Kuma ya amsa cewa babban nufin su shine kashe wannan malamin,wato maulana Masoud sai dai abinda ba'a sani ba har yanzu ko suna nan warwatse

XS
SM
MD
LG