Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Bindiga Ya Kashe Yahudawa 11 A Wurin Ibadar Su


Jami'an FBI

Wani mutumin da yake ihu yana cewa, duk wadannan Yahudawa yakamata su mutu, ya shiga wani wurin bautar Yahudu a Pittsburg a jiya Asabar, ya fara harbin kan mai uwa da wabi ya kashe mutane 11, kuma wannan ne kisar bindiga na baya a nan Amurka.

Wasu mutane shida da suka yi yunkurin kama maharin ciki har da dan sanda, sun samu rauni a cewar jami’an da suka bayyana cewa wasu fararen hula su biyu suna cikin mawuyacin hali.

Da alamar wannan shine mummunar hari da aka taba kaiwa al’ummar Yahudu a tarihin Amurka, a cewar wata kungiyar Yahudawa mai zaman kanta a Amurka.

Hukumar binciken manyan laifuka a Amurka ta FBI, ta fara gudanar da binciken wannan harbin da aka yi shi cikin tsano.

Babban jami’in hukumar FBI a Pittsburg, Bob Jones ya fadawa manema labarai cewa, basu da wata masanaiya a kan ko jami'an tsaro suna da bayanai a kan wanda ya yi harbin, kafin ya kai harin na jiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG