Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Kato da Gora Ya Tsere Daga Bama Zuwa Tudun Tsira


Dan Kato da Gora ko Civilian JTF.

Wani dan kato da gora wanda ya ki ya bayyana sunansa sabili da dalililan tsaro yace ya gudo daga garin Bama ranar Litinin da ta gabata yayin da 'yan kungiyar Boko Haram suka mamaye garin.

Shi dan kato da goran da ya tsere daga Bama zuwa Abuja ya bar iyalinsa a garin Baman. Katinsa na zama dan kato da gora ya taimakeshi tsallake shingayen sojoji.

Dan Kato da goran yace dabarun hatimin siri ko surkulle ba zasu iya kare 'yan kungiyar kato da gora daga 'yan kungiyar Boko Haram ba. Yace an basu asiri iri iri kuma da yaddar Allah makami ko harbin bindiga baya kamasu sai dai idan kwana ya kare. Amma yace ya gudu ne domin idan 'yan Boko Haram suka ga harbi ko makami ba zai kamaka ba sai su taka mutum da mota.

Yayin da wasu ke kauracewa wasu sassan Borno tsohon gwamnan jihar Ali Modu Sheriff da aka zarga da daukan nauyin Boko Haram ya shirya tsaf domin shiga Maiduguri yau. Sheriff dai ya shige cikin PDP tsundum da nuna hakan ne zai dawo da salama a arewa maso gabas.

Tsohon kwamishanan jihar Borno Inuwa Vala shi ne babban jami'i labarun Ali Modu Sheriff. Yace Modu Sheriff na shirin komawa Borno amma sun ji akwai wasu 'yan tasha da aka shirya su yi rashin hankali. Sun gayawa jami'an tsaro idan wani kuma yayi rashin hankali akwai doka. Kada a tada masa hankali domin baya neman tashin hankali da kowa.

Akan wai Ali Modu Sherif ya fi son ya zauna a tudun mun tsira maimakon ya zauna a Maiduguri sai Inuwa yace kasuwanci yake yi a Chadi kuma baya son a zargeshi da yiwa gwamnatin jihar katsalandan.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG