Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Nijeriya Sun Yi Galaba Akan 'Yan Boko Haram a Garin Konduga


Wasu sojojin Nijeria a bakin aiki

Ga dukkan alamu sojojin Nijeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram a garin Konduga, su ka kashe na kashewa tare da kwace muggan makamansu. Wannan ya kwantar ma mazauna birnin Maiduguri da kafin nan ke fargabar yiwuwar 'yan bindigar su abka ma birnin

Tun jiya ake ta samun rahotanni daga shaidun gani da ido na gagarumar nasarar da ake ce sojojin Nijeriya sun yi kan ‘yan kungiyar Boko Haram a garin Konduga, inda bayan sun fatattaki na fatattaka sun kuma kashe na kashewa, sojojin Nijeriya sun kuma kwace muggan makamai da motocin yaki har da na kaca daga wurin ‘yan Boko Haram.

Shaidun gani da ido sun shaida ma Muryar Amurka cewa dinbin ‘yan Boko Haram din sun gamu da ajalinsu ne bayan da sojojin Nijeriya da ke fama da suka su ka yi kukan kura su ka cire tsoro su ka far ma mayakan na Boko Haram. Wannan nasarar da sojojin Nijeriya su ka samu kan Boko Haram ta dadada ma mazauna birnin Maiduguri, wadanda kafin nan ke cike da tsoron yiwuwar ‘yan Boko Haram din su abka ma birnin kamar yadda aka yi ta yada jita jitar yiwuwar faruwar hakan.

Kodayake ya zuwa yanzu hukumar sojin Nijeriya da ke Abuja ba ta ce komai ba akan wannan al’amarin na hallaka mayakan sa kai fiye da 80, amma kakakin Bataliya ta 7 ta sojojin Nijeriya Kanar Usman ya tabbatar da faruwar abin amma ya ki yin cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi: Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram

XS
SM
MD
LG