Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani gungun mahara ya kai hari kan masu gadi a tashar jirgin saman Damokaradiyar Jamhuriyar Congo


Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suna sintiri a Damokaradiyar Kongo.

Wani gungun mutane dauke da makamai ya kai hari kan sojojin dake gadin wata tashar jirgin sama a Damokaradiyar janhuriyar Congo .

Wani gungun mutane dauke da makamai ya kai hari kan sojojin dake gadin wata tashar jirgin sama a Damokaradiyar jamhuriyar Congo da asubahin yau jumma’a. Kakakin gwamnati yace an bude wutar ne a tashar jirgin sama ta Lubumbashi dake yankin Katanga inda ake hakar mu’adinai, da misalin karfe hudu na asuba agogon kasar. Kamfanin dillancin labarai na AP yace an kashe wani mai gadi farin kaya bisa ga cewar wani dake zaune a yankin da ya nemi a saya sunansa. An hakikanta cewa kungiyar ‘yan tawaye mai da’awar ballewa ce ta kai harin, sai dai kakakin yace ba a tantance ‘yan bindigan ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG