Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Yi Zaben Fidda Gwani a Nijar


Wata mace take rike da katin kuri'a a wata rumfar zabe a Niamey,babban birnin Nijar.

Jami’an hukumar zaben kasar jamahuriyar Nijer sun ce dadadden dan hamayyar kasar Mahamadou Issoufou ne a sahun gaban zagayen farkon zaben shugaban kasar bayan an kidaya akasarin kuri’un da aka kada.

Jami’an hukumar zaben kasar jamahuriyar Nijer sun ce dadadden dan hamayyar kasar Mahamadou Issoufou ne a sahun gaban zagayen farkon zaben shugaban kasar bayan an kidaya akasarin kuri’un da aka kada.

Shugaban hukumar zaben kasar, Abdourahmane Ghousmane ya fada cewa Mahamadou Issoufou ya samu sama da kashi 36 cikin dari na kuri’un da aka kada a zaben da aka yi ranar litinin. Ya ce dan takarar da ya zo na biyu shi ne tsohon frayim minista Seini Oumarou.

Su ne za su kara a zagaye na biyun da za a yi.

‘Yan takara goma ne su ka shiga zaben, a cikin su har da na kurkusa da tsohon shugaba Tandja Mamadou da aka yiwa juyin mulki, wanda yanzu haka ya na kaso bisa zargin azurta kai ba bisa k’aida ba.

A cikin watan fabarairun shekarar dubu biyu da goma sojojin kasar jamahuriyar Nijer su ka hambare Mr.Tandja daga mulki, bayan da ya tilasta yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar domin ya karawa kan shi iko ya kuma tsawaita wa’adin mulkin shi bayan shekaru goma.

Zaben na ranar lahadi ya hada har da na ‘yan majalisar dokoki. ‘Yan kallon zabe daga Tarayyar Turai da kungiyar kasashen Afirka sun ce zaben ya gudana cikin nasara, duk da wasu mishkilolin da aka fuskanta.

Zaben na ranar litinin cikon alkawarin da sojoji su ka yi ne cewa za su maida kasar ga mulkin farar hula.

Jami’an hukumar zabe sun ce wadanda su ka yi rajistar zabe a kasar sun miliyan 6 da dubu dari 7, amma kimanin rabin wannan adadi ne ya fita kada kuri’a a zaben na ranar litinin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG