'Yan sanda a Afghanistan, sun ce, wani harin kunar bakin wake rataye da bam, a kusa da wata makarantar horar da sojoji a Kabul, ya kashe a kalla jami’an tsaro shida, wasu 16 kuma sun jikkata.
Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar, ta tabbatar da harin bam din, na yau Alhamis a bakin kofar jami’ar Marshal Fahim National Defense, da ke babban birnin kasar, amma ba ta bada karin bayani ba.
Wasu jerin hare-hare da aka kai kwanan nan a Kabul, sun kashe mutane da dama, ciki har da wani babban malamin addinin Islama.
Sojojin Afghanistan, sun kai farmaki a wata cibiyar tsare mutane ta ‘yan Taliban, a kudancin lardin Zabul, dake fama da tashin-tashina, inda suka sako 'yan fursunoni 18, ciki har da jami’an tsaro 12.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 24, 2021
An Ceto Ma'aikata 11 Daga Wata Mahakar Zinari a China
-
Janairu 24, 2021
'Yan Sanda Sun Kama Dubban Masu Zanga Zanga A Rasha
-
Janairu 23, 2021
Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Duniya Ya Doshi Miliyan 100
-
Janairu 17, 2021
Wani Ayarin Baki Masu Kaura Na Dosar Amurka Daga Honduras
-
Janairu 16, 2021
India Ta Kaddamar Da Shirin Bada Riga Kafin COVID-19
-
Janairu 11, 2021
WHO Za Ta Aika Wata Tawagar Bincike China
Facebook Forum