Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Na Hannun Daman Trump Ka Iya Huskantar Takunkumin MDD Kan Shiga Makamai Libya


Antonio Guterres
Antonio Guterres

Wani dan kwangilar tsaro mai zaman kansa kuma na hannun daman tsohon shugaban Amurka Donald Trump Erik Prince ya take dokar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta haramta shiga da makamai a Libya, da masu binciken MDD suka gano da kuma kafafen yada labaran Amurka suka yada jiya Juma’a.

Jaridun New York Time da Washington Post ne suka bankado wannan rahoton sirri na kwamitin sulhun MDD, cewa Prince ya shiga da sojojin haya na kasashen waje da kuma makamai zuwa ga Khalifa Haftar, wanda ya yi yakin hambarar da gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD a shekarar 2019.

Aikin na dala miliyan 80 ya hada da shirya rundunar kai manyan hare hare da zasu gano su kuma kashe kwamandodin Libya masu adawa da Haftar, cikin su akwai ‘yan kasashen Tarayyar Turai, a cewar jaridar New York Times.

Prince tsohon sojan ruwan Amurka kuma dan uwan sakataren ilimi na gwamnatin Trump Besty Devos, shine shugaban wani kamfanin tsaron mai zaman kansa na Blackwater, wanda ake zargin ayyukansa da kashe fararen hula ‘yan kasar Iraqi da basu da makamai a Bangladesh a shekarar 2017.

Zargin da ake yiwa Prince ka iya jefa shi cikin yiwuwar huskantar takunkuman Majalisar Dinkin Duniya, a cewar Times.

Prince bai bada hadin kai ga binciken MDD kana lauyoyin sa sun ki magana da jaridar ta New York Times.

Haka zalika bukatar neman bayani da kamfanin dillancin labaran AFP ya shigar wa wani kamfanin Hong Kong da Prince ke cikin kwamitin darektocinsa kuma mataimakin shugaban kwamitin, hakan bai samu ba.

XS
SM
MD
LG