Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani rikicin addini ya yi sanadin mutuwar mutane hudu a garin Tafawa Balewa na jihar Bauchi


Wadansu mutane tsaye kusa da wata mota da aka koma a kofar wata majami'a a birnin Maiduguri , (File)

‘Yan sanda a jihar Bauchin Najeriya sun ce wani rikicin addini da ya barke ya yi sanadin kashe mutane hudu.

‘Yan sanda a jihar Bauchin Najeriya sun ce wani rikicin addini da ya barke ya yi sanadin kashe mutane hudu. Kwamishin ‘yan sanda na jihar Mohammed Indabawa, yace rikicin ya sami asali ne daga wata gardama da ta barke a wajen wani wasan sunuka a garin Tafawa Balewa, wanda ya rikide ya zama fadan addini tsakanin matasa Kirista da kuma Musulmi. Fadan ya yi sanadin kona wuraren ibadar Musulmi da kirista da dama. Jami’ai sun ce an fara tashin hankalin ne jiya Laraba da yamma ya kuma ci gaba yau Alhamis kafin ‘yan sanda su shawo kanshi.

XS
SM
MD
LG