Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kishin Islama ne sun kashe Soja a Najeriya


'Yan sandan kwantar da tarzoma na Najeriya

Wasu 'yan kishin Islama sun wani kashe Soja a Maiduguri

Wadansu ‘yan bindiga sun kashe wani soja a arewacin Najeriya jiya Lahadi, harin da hukumomi suka ce kungiyar Islaman nan mai tsatsauran ra’ayi Boko Haram ce ta kai. Bisa ga cewar hukumomin, ‘yan bindigan da ba a tantance ba, sun harbe suka kuma kashe sojan kusa da wata majami’a a birnin Maiduguri. Wani kwamandan soji yace sojan yana sintiri ne a unguwar tare da sauran sojoji aka kashe shi jim kadan bayan rabuwarsu da sauran abokan aikinshi. Ana dorawa membobin kungiyar Boko Haram alhakin hare hare da dama da aka kaiwa ‘yan sanda da kuma shugabannin al’umma. Kungiyar ta sake bullowa bayan arangamar da tayi da ‘yan sanda da kuma sojoji cikin watan Yuli shekara ta dubu biyu da tara, da tayi sanadin kashe kimanin mutane dari bakwai.

XS
SM
MD
LG