Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Al’umomi a Arewacin Najeriya Sun Fito Da Sabon Salon Kare Kai Daga Yan Bindiga


Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara
Yan Bindiga Barayin Shanu A Zamfara

A Najeriya al'ummomin da ke fama da rashin tsaro sun fara kulla kawance domin kare jihohinsu daga barazanar ‘yan ta'adda.

Al'ummar jihar Kebbi, a yankin Zuru ne suka fara kawance da takwarorin su na yankin Zamfara domin tsaron yankunan su daga masu satar mutane.

Zugu gari ne dake cikin yankin Bukkuyum ta jihar Zamfara, wanda ke makwabtaka ta yankin Wasagu na masarautar Zuru, kuma gari ne mai fama da matsalar ‘yan bindiga kamar yadda mazauna yankin suka shaidawa Muryar Amurka.

Bisa wannan dalilin ne kungiyar sa kai wajen samar da tsaro ta masarautar Zuru take ganin ko ta tsare yankin ta idan makwabta na da matsala to da sauran rina a kaba.

Kan haka ne, kungiyar ta fara kulla hulda da takwarorinta na makwabtan jihohi don samar da tsaro ta sahihiyar hanya, amma ta soma ne da yankin na Bukkuyum kamar yadda shugaban kungiyar ta Zuru Mani John ya bayyana.

A daya bangare kuma, duk da yake kungiyar ta sa kai ta Zuru na ikirarin tana taimakawa ga samar da tsaro, wasu Fulani ‘yan asalin yankin na Zuru suna ganin kamar tana sauke da fushinta ne a kan su.

Umar Abubakar, dan asalin yankin Bena ne amma yanzu ya ce ya yi kaura daga yankin saboda yadda ake zallazawa fulani a yankin. To sai dai jagoran kungiyar ta ‘yan sa kai ya ce ba haka abin yake ba.

Ya zuwa yanzu dai yankunan da suka nuna sha'awa yin kawance da yankin na Zuru wajen taimakawa tsaro sun hada da Gummi da Sakkwato ta shiyar Tureta da Niger da Yauri Shanga da kuma Bagudo, abin jira a gani shine tasirin da kawancen zai yi wajen taimakawa tsaro a dukkanin yankunan.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00


XS
SM
MD
LG