Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Al’umomin Najeriya Sun Fara Yin Fito-Na-Fito Da ‘Yan Ta’adda


A Najeriya kasancewar matakan da gwamnatoci ke cewa tana dauka na dakile ayukkan ta'addanci ba sa hana al’amarin gudana ba, al'umomi sun fara samun kwarin gwiwar yin fito-na-fito da 'yan ta'addar har da samun galaba.

Ganin cewa kokarin da hukumomi ke yi wajen shawo kan matsalolin rashin tsaro ba sa hana ‘yan bindiga yin aika-aikarsu ba, musamman a Arewa maso yammacin Najeriya, yanzu jama'a sun fara kosawa har sun fara tunkarar ‘yan bindigar da kan su.

Karin bayani akan: Sokoto, Sanusi Abubakar, Nigeria, da Najeriya.

Irin wannan ne ya faru a garin Gidan Buwai da ke Sokoto inda ‘yan banga wadanda ke taimakawa jami'an tsaro suka yi musayar wuta da barayin shanu kuma suka kashe mutum shida daga cikinsu a cewar shugaban kungiyar ta 'yan banga.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ASP Sanusi Abubakar ya tabbatar mana da aukuwar lamarin.

A dalilin irin wadannan matsalolin ne ya sa wasu al'ummomi a jihar suka yi taron addu’o’i don kai kukansu ga Allah ya kawo saukin wadannan musifu.

Mutanen sun shafa mako daya suna saukar Alkur'ani tare da wasu addu'o'i na musamman.

Yayin Wata tattaunawa da Muryar Amurka wasu daga cikin mutanen yankunan sun ce idan mutum ya yi iya kokarinsa amma ya gaza, to sai ya koma ga rokon Allah.

Wannan kira na su dama abu ne wanda tun tuni malaman Musulunci suka dade suna shawarar ‘yan Najeriya da a koma ga Allah domin neman mafita daga wadannan musifu.

Saurari rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00


Dubi ra’ayoyi

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG