Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Dalibai Mata Sun Kamu da Cutar Kanjamau Sanadiyar Tarawa da Malaminsu


Jihar Adamawa

Wani malamin a makaranta ya sawa wasu dalibai mata cutar kanjamau a jihar Adamawa

An dade ana zargin wasu malamai da yin lalata da dalibansu.

To amma mafi muni shi ne na malaman dake dauke da kwayar kanjamau da suke tarawa da dalibansu.

Dubun wani malamin da ya sha yin lalata da dalibansa ta cika. Malamin yana koyaswa ne a makarantar Tafari-Ganye Community Islamic Center kuma asirinsa ya tonu ne bayan da aka samu daya daga cikin dalibansa tana dauke da kwayar cutar kanjamau. Bayan da iyayenta suka tsananta mata suka gano cewa tayi lalata ne da malaminta.

Tuni 'yansanda suka cafke malamin kuma suna cigaba da bincikensa domin gano dalibai nawa ne lamarin ya shafa. DSP Usman Abubakar kakakin 'yansandan yayi karin haske. Yace duk wadanda suka san yana yin aika aikar su fito fili su fada musamman 'yan matan da ya taba yin lalata dasu.

Iyaye yanzu sun tashi suna cewa dole ne a sa ido akan makarantu da malamansu. Abun bakin ciki ne a ce malaman dake koyas da yara su ne kuma suke lalata dasu. Yakamata tun kafin a dauki mutum aiki a tantance shi a san wane irin mutum ne. A san halayrsa wadda idan ya zo ba zai cutar da dalibai ko mutane ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG