Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Hare-Hare Sun Halaka Mutum 63 A Najeriya


Wasu sojojin Najeriya a Maiduguri
Wasu sojojin Najeriya a Maiduguri

Hare-haren na yammacin Jumma’a a garin Damaturu sun wakana ne bayan tashin dimbin boma-bomai da safe a garin Maiduguri

Kungiyar agajin jin kai da taimakon gajiyayyu ta Red Cross ko Croix Rouge tace mutane 63 a kalla sun mutu a arewacin Najeriya bayan wasu jerin fashewar boma-bomai da harbe-haebe a garin Damaturu na jahar Yobe.

‘Yan bindiga sun kaiwa garin hari da yammacin jiya Jumma’a, su ka farfasa boma-bomai a ofisoshin ‘yan sanda, da wani banki da kuma Coci-Coci da dama. An kwan dare ana barin wuta a garin, har ya zuwa safiyar yau asabar.

Haka kuma ‘yan bindigar sun kai hari kan wani kauyen da ke Poktiskum, inda suka kashe mutane biyu a cewar shaidun gani da ido.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare-hare. Amma mazauna yankin sun dora laifin a kan ‘yan Boko Haram wadanda suka sha kai hare-hare a arewacin kasar ta Najeriya.

Har yanzu gwamnati ba ta ce komi ba akan wadannan hare-hare.

Hare-haren na yammacin Jumma’a a garin Damaturu sun wakana ne bayan tashin dimbin boma-bomai da safe a garin Maiduguri da ke kusa da Damaturu. Mutane da yawa sun ji ciwo, amma har yanzu babu tabbas game da adadin wadanda suka mutu a cikin harin.

Duka wadannan hare-hare na Maiduguri da Damaturu sun wakana a cikin watan Dhul-Hijjah, ana sauran kwana biyu a yi sallar layya.

Aika Sharhinka

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG