Accessibility links

Bama-Bammai Ukku Sun Tashi A Maiduguri

  • Aliyu Mustapha

Police officers armed with AK-47 rifles stand guard at sandbagged bunkers along a major road in Maiduguri, Nigeria.

Akalla bama-bammai ukku suka tagshi Jumu’ar nan a Maidugurin jihar Borno ta Nigeria

Jami’ai a Nigeria sunce akalla bama-bammai har guda ukku suka tashi yau Jumu’ar nan a garin Maidugurin jihar Borno. Shedu sun ce bama-bamman sun tashi daya bayan daya ne a wannan garin dake fama da tashin hankali inda kuma gwamnati take dora laifin rigimar akan kungiyar ‘yan Boko Haram. Hukumomi sunce daya daga cikin bama-bamman ya tashi ne a wata makaranta inda jama’a suka taru don sallar Jumu’a. Jami’an tsaro kuma sunce bam na biyu ya tashi ne a cikin wani gida, mazaunin ma’aikatan tsaron da aka baiwa aikin kare lafiyar garin na Maiduguri daga ‘yan Boko Haram din. har zuwa yanzu dai ba’a fayyace ko an sami asaran rayukka a lamarin ba. A jiya Alhamis sojoji suka fara bin gida-gida, suna binciken neman makamai.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG