Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kusoshin APC Na Jihar Adamawa Sun Koka da Yadda Gwamnan Ke Ciwo Bashi


Jihar Adamawa
Jihar Adamawa

Yanzu haka a Jihar Adamawa, an fara ta da jijiyar wuya game da basussuka da ake zargin sabuwar gwamnatin gwamna Sanata Muhammadu Umaru Jibrilla Bindo ke karba domin gudanar da wasu hidimomin jihar.

Wannan ma ko ya biyo bayan rancen da gwamnan jihar ke cigaba da karba ne duk da cewa ma’akatan jihar suna kukan rashin samun albashisu.

Gwamnan Senata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla ya kare muradun gwamnatinsa ta kashe kudaden ke yi, kuma wannan ma na zuwa ne yayin da jam’iyun adawa da kuma wasu kusoshin jam’iyarsa ta APC,ke nuna damuwa da yadda gwamnatinsa ke ciwo bashi akai akai,lamarin da suke gani ka iya durkusar da asusun gwamnatin jihar.

Yayin da majalisar dokokin jihar ke sake amincewa gwamnan ya sake karban wani rancen kudi har fiye da nera biliyan biyar,tuni , wasu kusoshin jam’iyarsa ta APC, irinsu Sardaunan Jimeta Alh.Muhammad Haladu ke yin tir,da kuma kokawa da cewa yawan karbar bashin zai iya karya tattalin arzikin jihar musamman idan ba a amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace.

Haladu Dan Kwai wanda ke cikin wadanda suka tallata gwamnan a lokacin zabe,yace ba da yawunsu wannan ke faruwa ba.

To sai dai kuma da yake maida martani,kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajo,yace ai gwamnan jihar waliyi ne,tun da akan ka’ida ake kashe kudaden duk kuwa da cewa wasu yan siyasan jihar na son a yi kashe mu raba.

Su ma dai,yan majalisar dokokin jihar da suke amincewa da a karbo bashin sun musanta zargin cewa yanzu sun zama yan amshin shata. Hon.Hassan Barguma dan majalisar dokokin jihar ne kuma ya musanta zargin.

XS
SM
MD
LG