Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya Biyar Ne Suka Ransu A Kamaru


 Marchin Barga babban sifeton rundunar 'yansandan kasar Kamaru
Marchin Barga babban sifeton rundunar 'yansandan kasar Kamaru

Yan fashi da makami sun yi wa tawagar Majalisar Dinkin Duniyar biyar a garin Koncha na jamhuriyar Kamaru da ke kan iyakarta da makwabciyarta kasar Najeriya da suka je yankin aikin shata kan iyakokin kasashen biyu.

Shata kan iyakokin kasashen na zuwa ne sakamakon hukuncin da kotun kasa da kasa ta duniya ta yanke zamanin shugaba Obasanjo don ya raba gardama kan wasu wurare kamar su Bakassi.

Mai Magana da yawun gwamnan jihar Adamawa Mr, Yohana Mathias ya bayyanawa ‘yan jaridu takaicin gwamnatin jihar kan abkuwar lamarin yana musanta rade-radi da ake yayatawa cewa Boko Haram ce ta kai harin. Ya tabbatar ‘yan fashi ne suka farma tawagar.

Wata majiya da bata amince a ambaci sunanta ba ta shaida wa Muryar Amurka cewa wasu gungun ‘yan fashi da makami biyu suka kaiwa tawagar hari sau biyu a jere bayan sun yi la’akari da cewa jandarmomi biyu kacal ke rakiyar tawagar.

SP Othman Abubakar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar Adamawa wanda ya tabbatar da abkuwar lamarin ya ce baya da masaniyar kan irin kariya da jami’an tsaron Kasar Kamaru suka baiwa tawagar da yake tawagar su ta raka ayarinta kan iyakarta kana ta dankawa takwarorinta na Kamaru.

Daga cikin wadanda suka rasa ransu a tawagar akwai mutanen kasashen Kenya, Kamaru, da Najeriya.

Ga Karin bayani daga rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00


XS
SM
MD
LG