Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Manyan Kasashe a Afrika Sun yi Tir da Kalaman Trump


Shugaban Amurka Donald Trump

Manyan kasashen Afrika uku mafi arziki a nahiyar – Nigeria, Afrika ta Kudu da Ghana - sun yi da kalaman Donld Trump.

Wadannan kasashen Afrika da suka hada da Najeriya, Afrika ta Kudu da Ghana - sun kira jakadun Amurka dake kasashensu don bayyana musu rashin jin dadinsu da kalamin batancin da ake zargin shugaban Amurka, Donald Trump, da ambatawa akan kasashen Afrika da wasu kasashe masu tasowa irin su Haiti da El-Salvador.

Su ma kasashen Haiti da Bostwana sun kira jakadun Amurka dake nasu kasashe, sun bayyana nasu jin takaicin kan wannan maganar maras dadi da Trump ya fada.

Shugaban na Amurka ya girgiza mahalarta wani taron da yayi a fadarsa ta White House inda aka ce an ji shi yana cewa, “me yasa muke barin wadanan mutanen “kaskantattun” kasashe suna zo mana kasarmu?”

Rahottani sunce Trump ya bayyana cewa ya fi son ganin mutanen kasashe irinsu Norway suna shigowa Amurka. Ko a kasashen Turai, kasar Norway fitacciya ce saboda kasar Turawa ce farar fata zallansu, yayinda kasashen da Trump ke nunawa wulakanci kuma suke na Bakaken Fata da masu ruwan launin kasa-kasa.

Rahottanin dake fitowa daga ciki da wajen Amurka na nuna cewa kasashen duniya da dama yanzu suna wa Amurka da shugabanta Trump kallon wadanda suka kama hanyar rungumar akidar wariyar launin fata.

Trump dai ya musanta cewa yayi wannan kalamin na batanci.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG