Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Sun Yi Zanga zangar Bukatar Kawo Karshen SARS a Abuja


Yawan gallaza ma jama'a da ake zargin 'yan sanda na musamman da ake kira SARS da yi, ya sa wasu matasa yin zanga zanga a gaban ginin shelkwatar ‘yan sanda da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da yin korafe-korafe game da kashe-kashe na ba bu gaira babu dalili da ake zargin rundunar ‘yan sanda ta musamman masu yaki da manyan laifuffuka wato SARS da yi.

Kiraye-kirayen neman a kawo karshen rundunar ‘yan sanda ta SARS ya kara kamari ne bayan bullar wani faifan bidiyo da ya nuna jami’an ‘yan sandan suna jan wasu mazaje biyu a kasa daga hotel har ta kai ga harbe daya daga cikin su a kan titi a jihar Legas, lamarin da ya kai ga sabunta kiran a kawo karshen SARS din gaba daya.

Zanga zangar #ENDSARS Aisha Yesufu
Zanga zangar #ENDSARS Aisha Yesufu

‘Yar fafutuka dake kan gaba-gaba a neman kubutar da ‘yan matan Sakandaren Chibok da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a watan Afrilun shekarar 2014, Aisha Yesufu, na daga cikin jerin masu zanga-zangar da suka bayyana a shelkwatar ‘yan sanda a Abuja, ta ce yakamata a dauki matakan da suka dace, domin kashe-kashen ya isa haka.

Jagoran gangamin neman juyin juya hali wato “Revolution Now” kuma mawallafin jaridar yanar gizo ta Sahara reporters, Omoyele Showore, ya mika bukatar a kawo karshen SARS sakamakon kashe-kashen matasa a bisa dalilin irin tufar da suka sanya, wayoyin da su ke rike da su, da kuma neman diyya wa iyalan wadanda ba-su-ji-ba, ba-su-gani-ba da suka rasa ransu a hannun ‘yan sandan.

Zanga zangar ENDSARS
Zanga zangar ENDSARS

Sanata Shehu Sani ya yi jawabi a kan dalilin fitowa zanga-zangar da aka yi, ya ce, SARS bangare ne na rundunar ‘yan sanda kuma ya kamata ace suna girmama dokar kasa.

Gwamnati dai ta baza jami’an rundunar ‘yan sanda ta musamman a yaki da manyan laifuffuka a fadin kasar wadanda yawancin lokaci ke aiki babu inifam ko cikakkiyar shiga irin ta jami’an tsaro, sai dai shiga wadda ba a san jami’an tsaro da ita ba.

Jarumai kamar su Falz, Wizkid, Davido sun shiga wannan gangamin neman a kawo karshen SARS inda gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sha alwashin daukar mataki cikin gaggawa a kan batun.

An kafa rundunar ta SARS a shekarar 1992 domin yaki da karuwar muggan laifuffuka. Saboda wadannan kiraye kiraye babban sufetan ‘yan sandan kasar ya dakatar da yawancin aikace-aikacen rundunar ta SARS.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00


Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG