Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mayaka Masu Alaka Da Kungiyar IS Sun Kashe Fararen Hula Akalla Goma Da Suka Hada Da Yara A Gabashin Kongo


Yan bindiga
Yan bindiga

Rundunar sojin Congo ta ce 'yan tawayen masu nasaba da tsattsauran ra'ayi sun kashe akalla mutane goma sha biyu a wani samame da suka kai a wani kauye a gabashin kasar, a tashin hankalin na baya bayan nan a kusa da kan iyaka da Uganda.

'Yan tawayen Allied Democratic Forces masu alaka da kungiyar IS sun dade suna kai farmaki a yankin kan iyaka. Majalisar Dinkin Duniya ta ce a makon da ya gabata an kashe kusan mutane 200 a wannan shekara.

Kaftin Anthony Mulushayi, kakakin rundunar sojojin Kongo a lardin Kivu ta Arewa, a ranar Talata ya ce maharan da safiyar wannan rana sun kona wani asibitin yankin tare da kora wasu fararen hula zuwa daji. Ya ce sojojin sun mayar da martani inda suka kashe hudu daga cikin maharan tare da ceto mutane hudu.

Wani shugaban farar hula na yankin, Kakule Mwendapeke, ya ce adadin fararen hula da abin ya rutsa da su ya zarta haka, inda aka kashe akalla mutane 17, ciki har da yara hudu ‘yan kasa da shekaru 10. Wasu mutane 15 kuma sun bace bayan an yi garkuwa da su, in ji Mwendapeke. Wadanda suka tsira sun tsere daga kauyukansu don neman mafaka a wasu biranen da ke kusa da su ciki har da Beni da Mangina.

Yankin na gabashin Kongo dai ya shafe shekaru da dama yana fama da tashe-tashen hankula yayin da sama da kungiyoyi 120 dauke da makamai ke fafutukar ganin sun mallaki albarkatun ma'adinai masu mahimmanci, wasu kuma na kokarin kare al'ummominsu. ‘Yan tawaye na yawan kashe jama'a. Rikicin ya sa sama da mutane miliyan bakwai kaurace wa gidajensu, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Bintou Keita, babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya a Kongo, ta yi gargadi a makon da ya gabata cewa tashe-tashen hankula na kara ta’azzara, inda aka samu rahoton cin zarafin dubban mutane da suka hada da fyade da cin zarafin mata a bana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG