Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Da Dama A Wasu kauyukan Jihar Filato


Hoton wani harin da aka taba kaiwa a garin Jos

Kai hare-hare kisan mummuke ya ki ci balle cinyewa a tsakanin kabilu a jihar Filato. Wanda ko a yau ma an sami wasu makamantan hare-haren da aka kai a wasu kauyukan jihar.

Hukumomi a jihar Filaton Najeriya sun tabbatar da faruwar wasu hare-haren da aka kai a wasu bangarorin jihar har aka sami asarar rayuka da dama.

Kamar yadda Kakakin rundunar tsaron jihar ta Filato Kaftin Ikedichi Iweha ya tabbatarwa da Wakiliyarmu Zainab Babaji a Jos. An sami wannan matsala a garin Kwata.

Haka kuma Zainab din ta zanta da Pakim Jacob daga kauyen na Kwata inda y ace an sami gawarwakin mutanensu akalla guda goma sha shida da aka samu a yashe.

Ya kara da cewa, wasu kimanin mutanen kauyen kimanin dari ana nemansu don kuwa sun yi batan dabo. Haka ma a daya bangaren a wani kauyen da ake kira Golhos da ke karamar hukumar Riyom an kashe akalla mutane hudu aka kuma dawo da gawar wasu guda biyu da suka cika a asibiti.

Kamar yadda wani da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana mata akwai mutane guda biyar a asibiti suna jinyar raunukar da suka samu. Ga rahoton nan cikin sautin kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG