Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015:Wasu sun Yanka Shanu da Awaki a Bauchi da Taraba


Wasu sun Yanka Awaki da Shanu dan Murna

Bukukuwa da farin cikin samun nasarar Janar Muhammadu Bahari na cigaba a jahohin Taraba da Adamawa.

Kamar yadda jama'a ke ta farin cikin kafa sabuwar gwamnatin da suka zaba ranar Asabar da Lahadin da ta gabata a wasu sassan Najeriya, haka take a jahohin Taraba da Adamawa.

Jama'ar wannan wuri na cigaba da bukukuwan nasarar da janar Muhammadu Buhari ya samu ta lashe zaben na 2015,

Duk kuwa da harbin da jami'an tsaro sukayi wa wani matashi a kafa a garin Jalingo na jahar Taraba yayin irin wannan murna. Haka ma rahotanni sun nuna cewar wasu jama'a sun rasa rayukan su a garin Maya Ballo a Jahar Adamawa kuma jami'in yada labaran karamar hukumar mai suna Malam Kabir ya tabbatar da aukuwar abin.

A cewar sa, "yara masu wasa da mashinne suka hadu a tsakiyar hanya wanda abin yayi sanadiyar rasuwar yara uku nan take, kuma yayin da sauran ke asibiti sakamakon raunikan da suka amu."

A garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram, jama'a sun shirya walima kamar yadda akayi a garin mubi da kwanakin baya 'yan kungiyar Boko Haram suka sanya wa suna Madinatul Islam.

Jama'ar wananan wuri da sun yanka shanu da awaki domin nuna farin cikinsu a wannan gagarumar nasarar da Janar Buhari ya samu.

Jama'ar wannan yanki dai sun fuskanci hare-hare da dama daga kungiyar Boko Haram, kuma suna farin ciki da wannan sabuwar gwamnati domin a cewar wani matashi, sun dade suna addu'ar ganin wannan lokaci kuma suna fatan hakan zai kawo karshen zubda jinin da kungiyar 'yan yakin sa kai ta Boko Haram ke yi a garuruwan.

ZABEN 2015:Wasu Sun Yanka Shanu da Awaki a Bauchi da Taraba - 2'34"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG