Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci A Canada


Masu aikin agajin gaggauwa a masallacin da aka kai hari.
Masu aikin agajin gaggauwa a masallacin da aka kai hari.

Wasun ‘yan Bindiga sun kai hari a wani masallaci dake birnin Quebec na Canada da yammacin jiya Lahadi, inda suka kashe mutane shida suka kuma raunata mutum takwas.

Wata mai magana da yawun ‘yan sanda ta ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hanu a harin, amma kuma ba ta bayyana asalin mutanen ko kuma dalilinsu na kai wannan hari ba.

Shugaban cibiyar harkokin addinin Islama a Quebec, ya ce ana salla da yamma ne aka kai wannan harin, sannan ‘yan sanda sun ce mutane 53 ne suke ibada a lokacin.

Firai Ministan Canada Justine Trudeau, ya yi Allah wadai da harin, lamarin da ya bayyana a matsayin “harin ta’addanci akan Musulmi”.

Ya kuma jaddada a wata sanarwa da ya fitar cewa kasar Canada na mutunta al’adar karbar baki da kuma nuna kauna ga kowane irin addini.

Trudeau ya kara da cewa, “Musulmin Canada na da matukar muhimmanci a kasarmu, kuma wannan irin wannan aika-aika ba shi da matsuguni a unguwanninmu da biranenmu da kuma kasar mu.”

A watan Yunin bara, an taba ajiye kan alade a kofar wannan masallaci da aka kai harin.

XS
SM
MD
LG